Labarai Namu
Zauren gidan yanar Labarai Namu:

Game da Labarai Namu

    ...Tayaya kake son a tunaka?
    ...Wane lokacine mafi baƙin ciki a rayuwarka?
    ...Me ka samu mafi alfahari?
    ...Yaushene farkon fara soyayyarka?

Amsa tanbayoyi yana taimakon mu wajen shirya labaran rayuwar mu. Yayin da muke magana, muna zama masu bada labari. Yayin da muke sauraro, za muji amon rayuwar mu kuma zamu gano sabuwar duniya ta hanyar wasu. Ta ƙarafafa masu bada labari da masu ganawa a duniya don rikodi da raba muryoyinsu akan layi, Labarai Namu™ yana nufin ƙirƙirar nasarar labaran rayuwar yau da kullun.

An kafa Labarai Namu ta UNICEF, Kwamfutar tafi da gidanka ga Yaro (OLPC), da Google, kuma don taimakon tattara, adana, da raba labaran kan layi na mutanen duniya da al'adunsu da al'ummarsu. Fasahar OLPC, mai tarayya da ayyukan UNICEF masu ci, yana bawa yara kayan aiki don ganawa, yin rikodi, da raba labaran iyayensu, kakanninsu, da wasu cikin danginsu da al'ummarsu. Abin mai da hankali yayin wannan dandalin shine game da ci gaban yara a manyan ƙasashe a Amurka ta Latin , Afirka, da Asiya inda kwamfutocin OLPC suka wadata. Daga baya, yara da wasu zasu sami damar raba labaran da suka yi rikodi kai tsaye ta Labarai Namu Gidan yara.

Hakanan Labarai Namu ya mai da hankali don bada damar zuwa labaran mutane daga cikin duniya acikin yarukansu. Kuma zaka iya jin labarai wanda aka tattara ta Gidan Tarihin Mutum a Barazil, da kuma ta UNICEF daga Ghana, Fakistan, Tanzaniya, da Uganda. Kuma muna tsammanin ƙara labarai daga Ajentina, Habasha, Najeriya, da wasu ƙasashe nan kusa.

Bincika taswira da menu na Nemo don jin labarai masu ban mamaki daga rayuwar yau da kullum na mutane a duniya.

Hakanan gidan Labarai Namu yana da Jagororin Ganawa kyauta don yara da manya. Koda kana yin rokodin ganawa don fasahar OLPC, fasahar tarihin baka kamar StoryCorps® (ɗayan ilhamominmu), ko don nasarar sirri, dangi, ko al'umma, waɗannan jagororin da gidan Labarai Namu zasu taimaka maka gano wannan ƙawatacciyar hanyar adana tunani don gaba.

Muna so ka raba muryarka, labaranka, da duniyarka, tareda Labarai Namu.

Saurari. Koyi. Rayu.

Ƙarin Albarkatun ƙasa

Bada labari shine zuciyar tarihin ɗan adam. Yawancin gidajen tarihi, gidan ajiya, laburare, jami'u da ƙungiyoyin al'dun gargajiya acikin duni suna tattarawa da adana tarihin baka don al'umma ta gaba. Yanzu, godiya ga fasahar rikodi ta zamani da ƙarfin Intanit don ajiyewa da raba abun ciki, ana samun damar yawancin wannan tarin akan layi. Labarai Namu yana tunƙahon haɗa ƙungiyoyin al'umma waɗandan suka bada sassauƙar hanya zuwa tarinsu bisa-yana.

Mai biyowa ƙaramin samfurine na albarkatun tarihin baka na duniya. Duk abinda zaka yi shine dubawa - da sauraro. Idan kana da wani tari wanda kafi so baka ganshi wannan lissafin ba, kada kaji nauyin faɗawa wasu gameda shi a Labardai Namu Ƙungiyar Google.

Zaɓaɓɓun Tarin Tarihin Baka

Ƙungiyoyin Zaɓaɓɓun Albarkatun & Tarihin Baka

Gida don Yara
Gida don Yara

Jagororin Ganawa
Ɗalibi | Baligi

Abokan Kafawa