Labarai Namu
Zauren gidan yanar Labarai Namu:

Tambayoyin da akeyi Akai-Akai

  1. Menene labarin Labarai Namu?
  2. Zan iya ɗora labarina zuwa Labarai Namu?
  3. Yaushe labarun ɗalibin OLPC zai wadata a wannan gidan?
  4. Me yasa akayi gidan yara na Labarai Namu da alamu?
  5. Makarantata zata iya shiga? Zamu iya samun kwamfutar tafi da gidanka na OLPC?
  6. Gidan tarihina na gida, laburare ko cibiyar tarihi sun ƙara tahinsu na baka zuwa Labarai Namu?
  7. Zan iya amfani da labarai a Labarai Namu saboda manufa tawa/ aiki?
  8. Akawai labaru don sauraro acikin yaruka da yawa?
  9. Labaru Namu suna da kayan aikin rikodi wanda zan iya amfani dasu?
  10. Menen na gaba don Labari Namu?

1. Menene labarin Labarai Namu?

Labarai Namu™ sabon aiki ne wanda ke ƙarfafa mutane don ganawa da abokai da masoya, da kuma raba waɗannan labaran tareda wasu. Abokan kafawarmu guda uku, UNICEF (www.unicef.org), Kwamfutar tafi da gidanka ga yaro (OLPC) (www.laptop.org), da Google (www.google.com), sun haɗu gaba ɗaya don taimaka ƙirƙira, rabawa, da haɓaka labaran sirri na duniya wanda aka tattara ta ganawar rikodi mai jiwuwa. Ɗalibai masu hanyar kwamfutocin OLPC nan kusa zasu sami damar shirya ganawa da raba su tare da wasu ta Labari Namu.

Munyi nufin haɗa labarai daga cikin duniya saboda munyi imani cewa kowa zai gano jin daɗi da ilhama cikin da yawancin waɗannan muryoyin, kalmomi da rayuwa mabambanta. Labarai Namu yana gamedalabarainaku.

2. Shin zan iya ɗora labarina zuwa Labarai Namu kai tsaye?

Ba yanzu ba. Koyaya, muna tsara samun salo acikin wuri a gaba don bawa mutane damar ɗora ganawarsu mai jiwuwa don rabawa. Kafin haka, haɗu da Jama'armu yanzu ta sauraron tarin labaranmu na yanzu samamme a Shafin Nemo Labari. Kuma yi amfani da damar jagororin ganawarmu don fara kama labara da rayuwar waɗanda ke kewaye dakai.

3. Yaushe labaran ɗalibi na OLPC zai wadata a wannan gidan?

Nan kusa, muna fata! Muna aiki da makarantu, masana fasaha, da ƙungiyar tarayya don bawa ɗalibai damar rikodin ganawarsu a kwamfutar tafi da gidanka sannan da ƙarasu zuwa tarin Labaru Namu. Duba sanarwa a zauren gidan yanar and on the Our Stories Gidan Jarida namu lokacin da labaran ɗalibi ya wadata don sauraro.

4. Me yasa akayi zauren yara na Labari Namu da alamomi?

Gidan yara naLabarai Namu an tsarashi musammam don nuna ƙwarewar amfani da kwamfutar tafi da gidanka ga yaro (OLPC). Waɗannan kwanfutar suna amfani alamomi fiye da haruffa da kalmomi don sanyata mafi sauƙi ga yara ako ina ( gami da waɗan sukayi ƙanƙanta da karatu) don yin abubuwa kamar ɗaukar hotuna da kunna kiɗa ta amfani da kwafutocin tafi da gidanka. Yara dake amfani da waɗannan kwamfutoci na iya ziyartar gidan Yara na Labari Namu don rabawa da jin labaran wanda wasu ɗalibai suka ƙirƙira, saboda muna so suji kamar suna gida a zaurenmu. Tsarin zane kuma yana tagazawa saƙonmu na ƙarfafa mutane na duk shekaru, yaruka, ilimi, da iko fasaha don raba labaransu na sirri.

Zaka iya karanta ƙari game da musaya mai alamar OLPC: http://www.laptop.org/laptop/interface/index.shtml.

5. Shin makarantata zata iya shiga? Shin zamu iya samun kwamfutar tafi da gidanka na OLPC?

Shirin kwamfutar tafida gidanka ga yaro (OLPC) ya dage don kawo kwamfutar tafida gidanka ga jama' ar ɗalibai a ƙasashe masu tasowa. Zaka iya koyan ƙari gameda yadda makarantun OLPC na farko suke amfani da kwafutar tafida gidanka ta ziyartar: http://www.laptop.org/children/learning/.

Ko wace makaranta tana maraba don amfani da Jagorar ɗalibi na Labarai Namu; koda yake an rubuta wannan tareda ɗaliban OLPC da kulawa, muna ƙarfafa malamai da ɗalibai ako ina don gano daɗin faɗin labari na sirri ta ganawa. Daga baya kuma, makarantun da ba na OLPC ba na iya ƙara rikodinsu zuwa tarin Labarai Namu kai tsaye (hakanan wasu ƙungiyoyi da mutane). Zamu sanar da waɗannan ayyukan a zaurenmu lokacin da suka samu. Kafin haka, muna ƙarfafa ɗalibai da malamai don jin labaran yanzu ya wadata a Labarai Namu ta zauren Nemo Labari.

6. Shin gidan tarihi na gida nawa, laburare, ko cibiyar tarihi sun ƙara tahinsu na baka zuwa Labarai Namu?

Bayanzu ba, amma nan kusa zamu sami hanya don ƙungiyoyi hakanan mutane don ƙara labaransu zuwa zaurenmu. Lokacin da waɗannan ayyukan suka wadata, zamu sanar taGidan Jarida namu dazauren gidan yana. Hakanan muna bada tarin hanyoyin haɗi ga ayyukan tarihin baka masu dacewa acikin duniya, da ƙaarfafa ka don tattauna tarin da kafi so da raba ƙwarewarka tareda wasu a Ƙungiyoyin Google na Labarai Namu.

7. Shin zan iya amfani da labarai mai juwuwa a Labarai Namu don manufata ko ayyuka?

Karanta Sharuɗɗan Sabi namu don ƙarin koyo game da abinda zaka iya yi da wanda baza ka iya ba tareda abun ciki gudana ta zauren Labarai Namu. An daidaita waɗannan sharruɗan amfanin daga Sharuɗɗan Amfani na YouTube saboda muna gudanar da mai jiwuwa ta amfani da mai kunna YouTube.

8. Shin akwai labarai don sauraro cikin yaruka da yawa?

Masu bada labari suna magana da yaransu na asali, don haka ganawa zata wadata cikin yaren da akayi rikodinta kawai. Wannan yana nufin, misali, labarai daga Gidan Tarihin Mutum a Barazil tabbas zasu zama cikin yaren Fotigis na Barazil. Bama juya ko fassara labarai masu jiwuwa don wasu yaruka, amma muna fatan samun wadatar muryoyi dayawa cikin yaruka dayawa nan kusa don kowa da kowa ya sami damar jin labarai cikin yarukansu.

9. Shin Labarai Namu suna da kayan aikin rikodi wand zan iya amfani dasu?

Yi haƙuri bamu da kayan aikin rikodi saboda masu amfani namu. Ɗalibai da suke amfani da kwamfutocin tafi da gidanka ga yaro (OLPC) suna da ginannen rikodin ciki da fasali na rabawa a kwamfutarsu ta tafi da gidanka wanda aka tsara don aiki tare da wannan aikin. Amma kowa zai iya rikodin ganawa don labari tareda na' urar rikodi ta asali kamar rikoda mai kaset. Mafiyawan kwamfuta suna da ikon yin rikodi. Jagorar ganawa na Manyaya ƙunshi shawarwari don rikodin ganawa ta amfani da waɗannan na'urori. Bugu da ƙari, in kana zaune cikin Amurka, kana iya samun ikon yin rikodi labari tareda taimakon StoryCorps® (ilhama don aikin Labarai Namu).

10. Menene na gaba don Labari Namu?

Wannan gidan da kake gani matakin farko ne kawai a doguwar tafiya, mai ban sha'awa. Nan kusa, ɗalibai tareda kwamfutocin tafi da gidanka ga yaro zasu samu dammar ƙara labaransu zuwa gidanmu. Daga baya, wasu makarantu, ƙungiyoyi, da mutane zasu sami damar raba labaransu ta Labarai Namu. Muna fatan zaka ziyarci gidanmu koda yaushe don kallo da sauraro lokacin da muka haɓaka tarinmu na muryoyin duniya da labarai wanda aka raba.

Gida don Yara
Gidan don Yara

Jagororin Ganawa
Ɗalibi | Baligi

Abokan Kafawa