Jagorar Ganawa na Ɗalibi
Wannan jagorar yana taimakon malamai da ɗalibai bincika duniyar bada labari na sirri ta ganawar tarihin baka. Ajujuwa masu damar kwanfutocin Tafi da gidanka zasu iya amfani da wannan jagorar don yin yawancin aikace-aikacen Labarai Namu, amma malamai da ɗalibai ko ina ana ƙarfafa su don koyo game da ganawa da yin rikodin tarihin baka ta wannan jagorar.
Game da Labarai Namu
Menene Labarai Namu
Sabon aiki ne wanda yake ƙarfafa mutane don ganawa da abokai, dangi, da wasu
a cikin al'ummarsu, da kuma raba waɗannan tarihin na baka tare da su. Abokan
kafawarmu guda huɗu, UNICEF (www.unicef.org),
Kwamfutar tafi da gidanka ga yaro (OLPC) (www.laptop.org),
da Google (www.google.com),
sun haɗu don taimaka ƙirƙirar, raba da haɓaka tarin labaran sirri na duniya,
wanda aka tattara ta ganawar rikodin sauti. Don ajujuwa, maid a hankalinmu
na farko yana kan bada fasaha da kayan aiki don ɗalibai masu amfani da kwamfutar
tafi da gidanka OLPC don yin rikodi da ganawar raba labarin sirri tare da wasu.
Don koyon ƙari game da abokan kafawa, ziyarci ɗakin abokai na Labarai Namu a www.ourstories.org/ourpartners.html.
Don koyo game da tsare-tsaren OLPC, ziyarci www.laptop.org.
Wane labari ne a bayan Labarai Namu?
Abokan kafawa sun haɗu gaba ɗaya kan maƙasudin ƙirƙirar cibiyar sadarwa ta duniya ta bada larai na sirri da masu sauraransu.
Munyi nufin haɗa labarai daga cikin duniya, saboda munyi imani cewa kowa zai gano jin daɗi da ilhama cikin da yawan waɗannan muryoyin mabambanta, kalmomi da rayuwa. Labarai Namu ya ƙunshi naka labarai.
Zan iya matsarwa da jin ganawar tarihin baka a gidan Labarai Namu?
Farkon sigar gidan Labarai Namu yana bawa masu ziyara dama don nemowa da jin
labarai daga Gidan Tarihin Mutun na Barazil, kuma daga Ghana, Uganda, Tanzaniya,
da Fakistan, wanda aka yi rokodi ƙarƙashin taimako da goyan bayan UNICEF. Waɗannan
labaran suna bada hotunan tilas na rayuwar yau da kullun, wanda mutane suka
yi rikodi yayin ganawa da juna kan batu kamar soyayya, yaƙi, iyayentaka, ƙuruciya,
aiki, imani, da wasu jigogi gama gari ga yawancinmu.
Sigar gaba ta gidan Labarai Namu zai baiwa ɗalibai damar amfani da kwamfutocin tafi da gidanka OLPC don raba labaransu tare da masu sauraro ta ƙara su zuwa gidan. Kuma a ƙarshe, mun tsara ƙarfafa wasu da yawa don raba labaransu ta gida namu.
Labarai Namu a cikin aji
Me ɗalibai zasu iya koyo daga ganawa ta labarin sirri?
Koya yana labarin da zai faɗa game da rayuwarsa.. Ta yin rikodi da raba su tare da duniya, ɗalibai zasu iya gina laburaren tunani da gogewa waɗanda suke nuna mana yadda kowanne yake fardi, amma kuma da kowanne.
Ta ganawa ta iyali da abokai, manya, malamai da wasu mutane masu bansha'awa, ɗalibai zasu I ya gano abubuwan mamaki game da mutanen da suka riga suka sani, da kuma game da inda suke rayuwa. Ta adanawa da raba waɗannan ganawar tare da al'umma, suna zama ingantattun abubuwan tarihi waɗanda ke taimaka faɗin labarin duk bil adama.
Amma, don ɗalibai, babban iko zai iya kasancewa cikin jin labarai masu yawo kuma na bazata game da wasu mutane, wurare, da gogewa.
Ta yaya malamai zasu yi aiki tare da ɗalibai kan wannan aikace-aikacen?
Bai taɓa zama wuri ba don koyar da iko da jin daɗin sadarwa ta gaskiya ba. Ƙarfafa koda murya mafi tsit don yin magana – don yin tambaya da amsa tambaya. Malamai zasu iya taimakon ɗalibai ta basu dama don gwada gwanintarsu ta ganawa, da ta taimakawa cikin gane mutane don ganawa, batu don tattaunawa, da tambayoyi don tambayawa.
Malamai zasu iya nunawa ɗalibansu cewa sauraro aikin sayayyane – kuma aikin koyone. Yana ƙarfafa yara da basu murya ta salon magana da takara, labari ɗaya alokaci guda. Taimaka watsa kalmar!
An tsara wannan jagorar don ɗaliban duk matakin shekaru waɗanda suke da ikon
yin tambaya da yin rikodin amsoshi. Don manya masu sauraro, muna Jagorar Ganawar
baligai, tareda ƙarin albarkatu, wanda aka daidai tashi daga kayan aikin da
aka ƙirƙira ta StoryCorps® (ilhama
don Labarai Namu), don taimakawa mutane a ko'ina yin rikodi da raba labaransu.
Yadda ake Shugabantar Ganawa
1. Zaɓi wani don ganawa
Nemo wani a cikin iyali ko al'umma wanda zai yuwu yana da babban labari da zai faɗa. Waye jaruminka? Waye ke faɗin labaran dariya? Wa kake son girmamawa ta sauraro?
Babu muggan zaɓuɓɓuka. Kawai tabbatar cewa mutumin da ake ganawa dashi yana jin daɗin magana game da kansa ko kanta, kuma bai damu da rikodinsa da ake yi ba. Wanda ake ganawa dashi ya fahimci cewa zai yuwa aji wasu suji labarin kuma a wadata shi don sauraro akan layi ta gidajen yanar sadarwa kamar Labarai Namu. Idan kayi tambaya mai kyau (duba samfur a ƙasa), dama itace, kuma zaka sami amsoshi masu bansha'awa.
Batun ganawa mai kyau ya ƙunshi...
- Mutanen dangi (iyaye, kakanni, ƙannan iyaye maza, ƙannan iyaye mata, ƴan'uwa)
- Abokan karatu da abokai
- Malamai da abokan shawara
- Shugabannin al'umma, almara da jarumai na gida
- Masu aikatawa, ƴantakara da ƴan kasuwa masu bansha'awa
- Masu ziyarar wajen gari tare da fardin ra'ayi
- Mapwabci, lafiyayyen ma'aikaci, kowane mutum acikin al'umma wanda ke da wani abu don rabawa
2. Gwajin gwanintar ganawa
Gwaji zai iya taimaka sanya saukin don ganawa da mutane; duk ƙarin gwaji yin tambayoyi (da sauraro), duk ƙarin jin daɗinka lokacin shugabantar ganawa ta "haƙiƙi". Anan akwai abin da zaka yi saboda gwaji don ganawa. Waɗannan jagororin suna da amfani don ganawa ta haƙiƙa, kuma.
A farkon ganawar:
- Nemi nitsattsen wuri Don ganawa, inda zaka iya magana da mutumin da kake ganawa ba tare da yawan hayaniyar bazata ba. A cikin gida ya fi. Nitsastsen ɗaki acikin gida, ko nitsastsiyar kusurwar aji zai yi aiki da kyau. Guji wuraren da kiɗa ko talabishin suke akunne a bango, ko inda wasu mutane ke kaiwa da dawowa cikin hayaniya.
- Bincika kayan aikin rokodinka,koda kana yin rikodi a kwamfutar tafi da gidanka, tare da mai rikodi mai lamba ko wata na'ura. Kunna ta kuma yi rikodin kanka da wanda zaka gana da kana faɗin"gwaji, gwaji, 1-2-3" kuma sannan ka sake kunna rikodin naka don tabbatar da cewa kkomai yana aiki dakyau, kuma cewa zaka iya jin kowane mutun sosai, ba tare da hayaniya daga baya ba.
- Nemi izini don yin rikodi da raba ganawar daga mutumin da ake ganawa da. Tabbatar cewa mutumin yana fahimtar cewa bayan rikodin labaransu, wasu zasu iya samun ikon jinsa. Kuma a tabbatar suna fahimtar cewa za'a iya samun labarin akan layi don sauraro ta gidan yanar sadarwa na Labarai Namu, ko wasu gidajen.
- Furta mahimmin bayani a farko zuwa "na farko" ganawar don zance na gaba. Wannan ya shafi rikodin sunayen mutanen biyu (sunayen farko suna kyau don yara), sheakaru, da, idan ya dace (kamar don kakanni da jikoko), alaƙarsu ga juna. Kuma ƙara wurin yanzu da kwanan wata da shekarar ganawar.
- Buɗe da ƴar magana don sauƙaƙawa mutumin da ake ganawar dashi cikin taɗi. Wasu lokuta faɗin kawai, "yaya kake yau?" ko, "An taɓa ganawa da kai game da labaranka da?" zai tamaki mai bada labari ƙarin jin nutsuwa.
- Zaɓi jigo ɗaya ko biyu don taɗi - kamar "Labaran ban dariya daga ƙuruciya," ko "Labarai game da dabbobin gida nawa." Wannan zai sauƙaƙa muku kai da mai bada labarin don maid a hankali kan batu ɗaya lokaci guda. Lokacin da ka zaɓi jigoginka, yi tunanin tambayoyin da zasu sanya mai ganawa magana, maimakon yin tambayoyin da za'a amsa su da "ee" ko "a'a". Don haka, misali, maimakon tambayar, "Kana da dabbobin gida lokacin da kake ƙarami?" ka iya cewa, "Bani labari game da dabbarka ta gida ta farko."
- Saita iyakar lokaci don ganawarka. Yafi kyau kawai a tsara ganawar labari zuwa minti 5 ko 10. Zaka iya samun ikon gama jigo ɗaya a wannan lokacin, kuma wataƙila ma biyu. Iyakance lokacinka yana sauƙaƙe maid a hankalin kan bada labari. Adadin tambayoyin da zaka iya yi a wannan ya dogara kan yawan yadda mai bada labarinka yake so ya faɗa. Don haka, idan mutumin da kake ganawa da yana gaya maka da yawa bayan kayi tambaya, bazai yuwu kayi tambayoyi da yawa ba. Idan mai baka labari ya bada gajerun amsoshi, zaka buƙaci ƙarin tambayoyi, don ka sa su baka labarinsu. Don taimaka maka sarrafa lokaci, yi amfani da agogon bango, agogon hannu ko wata na'urar aje lokaci (idan zaka iya) saboda ka iya zama cikin iyakar lokacinka. Amma idan ganawar tana tafiya daidai, saki jiki ka ƙara wasu mintuna 5 ko 10 ga taɗinka. Kawai ka tuna, ba zaka sami sassauƙar hanya don yanke ƙarin abun ciki ba, don haka duk abinda kayi rikodi wasu zasu ji ta daidai hanyar da aka yi rikodinsa, ba tare da daidaita komai ko ƙari daga baya ba.
Yayin ganawar:
- Yi ƙoƙari kar ka katse ko surutu lokacin da mutumin da kake ganawa dashi yake magana. Bari su amsa tambaya a nitse kamar yadda suke so kafin ci gaba.
- Jim ko murmushi don ƙarfafa abokin ganawarka, maimakon faɗin "uh-huh" ko wasu abubuwa waɗanda maiyuwa su katse taɗin.
- Tafi tare da bibiya ta barin ɗaya mutumin ya jagoranci taɗin, kuma yi magana game da abinda yake muhimmi ko abin sha'awa ko burgewa gare shi ko gare ta.
- Guji amsoshin "ee ko aa" ta yin tambayoyi waɗanda ke buƙatar ƙarin bayani. Misali, "Kana son zama dakta" zai iya haifar da sassauƙar amsar "ee". Madadin haka, tambayi "me yasa ka zama dakta?"
- Watsi da shiryayyun tambayoyinka idan taɗin yana tafiya cikin sabuwar manufa, amma ƙoƙarta ka zama tare da zaɓaɓɓun jigoginka. Kuma yi ƙoƙari ka ajiye iyakance lokacin da ka saita sanda ka fara(ko da yake zaka iya ƙara lokacinka idan ganawar tana tafiya daidai).
- Yi tambayoyin bibiya waɗanda suka shafi motsa rai da ji ajiki, kamar “Ya wannan yasa kaji?”
- Tambayi don dalla-dalla a tambayoyinka, kamar “Me gidanku suke nomawa a lokacin?” ko “Waɗanne launuka mahaifiyarka yawanci ta saka?” da sauransu.
A ƙarshen ganawar:
- Ƙare da "tambayar" rufewa wacce ke taimakawa mai ganawa dakai cika labarinsa ko labarinta, kamara “Akwai sauran wani abu da kake son ka gaya min?” ko “Akwai abinda na manta ban tambaya ba?” etc.
- Godewa wanda ka gana dashi don lokacinsu; idan abinda suka gaya maka ya motsa ka ko baka sha'awa, zaka iya sakin jiki ka raba abubuwan da kake ji tare da su. Saboda kawai an gama ganawa baya nufin baza ka iya ci gaba da magana ba!
3. Shugabanci ganawar
Yanzu lokaci yayi don ganawa ta ainihi! A ƙasa akwai samfurin tambayoyi. Amma ka iya shirya sabbin tambayoyi, kuma. Mafi kyawun tambayoyin da amsoshin na ba zata ne, kuma suna zuwa da kansu yayin taɗinku.
Tambayoyin da aka bada shawara don baligi:
- Gaya min wani abu game da kanka...
- Me rayuwa ta koya maka?
- Wanene da menene yayi maka ba zata a lokacin? rayuwarka?
- Me kake gain a rayuwarka nan gaba?
- Menene kafi alfahari dashi?
- Me kake da na sani?
- Kana da dabbobin gida lokacin da kake tasowa? Idan akwai, me sukai kama dashi?
- Yaushe ne mafi farin cikin rayuwarka? Mafi baƙin ciki? Mafi abin tunawa?
- Me kake son yi kayaushe, amma har yanzu bakai ba? Kana tunanin zaka sami dama kayi shi?
- Tayaya kake son a tunaka?
Tambayoyin da aka bada shawara don ganawa da saurayi:
- Waɗanne mutane ne mafi mahimmanci a rayuwarka?
- Wane ɓangaren makaranta kafi so?
- Menene abin tunawarka na farko?
- Kwatanta wurin da kake rayuwa – yaya can yake?
- Menene manyan burikanka a rayuwa?
- Wanene babban abokinka? Me kuke son yi tare?
- Kana da wasu ƴan uwa? Yaya sukai kama da kai kuma ta yaya suka bambanta?
- Menene fatanka ga yaran ƙasarku?
- Me kake son zama a gaba kuma me yasa?
- Kwatanta ranar yau da kullun a rayuwarka, daga sanda kake tashi har zuwa lokacin da kake tafiya bacci
5. Lissafa bayanin ganawar
Ɗalibai (ko malamai) zasu shirya bayanin cikin takarda game da kowacce ganawa don zance na gaba. Wanna zai sauƙaƙe nemo ganawar lokacin da aka ƙara ta zuwa tarin kan layi kamar Labarai Namu. Bayanin zai ƙunshi:
- Cikakkun mahimman bayanan ganawa kamar sunanka da sunan mutumin da ka gana dashi; kwanan wata da wurin da kayi rikodin ganawar; da, idan ya dace, menene alaƙarka da mai bada labarin (kakarka ce? ɗan'uwanka ne? malaminka ne?)Bayanin kula: karanta sashi na gaba, wanda ya tattara halayen da acikinsu maiyuwa baza ka so yin rikodin sunan mai bada labari ba.
- Mabuɗin batun al'amura waɗanda aka tattauna, kamar "Darasussukan rayuwa," "Yadda na haɗu da mahaifiyarka," "Labarun dabbobin gida," etc.
- Sunayen wurare, mutane, sha'ani ko wasu cikakkun bayanai da aka tattauna a ganawar.
- Kimanin tsayin ganawar (a mintuna). Galibi mintuna 5 - 10 sune duk abinda zaka so don yin rikodi, amma ajiye bayanan kula game da lokacin da ka fara da lokacin da ka tsaida rikodi.
- Sunan fayil ɗin ganawa, don a binciko shi da gano shi a gaba, idan rikodin na dijital ne.
- Idan anyi rikodin ganawar a kaset mai juwuwa, yiwa kaset ɗin alama da sunan mai ganawar/wanda aka gana dashi da kwanan watan ganawar. Alkinta kaset ɗin a amintaccen wuri kuma bushasshe idan zaiyuwu.
- Idan anyi rikodin ganawar a wani mai jarida na dijital ba kwamfuta ba, canjawa rikodin wuri zuwa kwamfuta (kuma haɗa da sunan mai ganawar da tarihin ganawar a cikin sunan fayil ɗin). Dabara ce mai kyau a ajiye kwafi a CD idan zaiyuwu, ko a adana kwafin ajiya a matuƙin faifai na waje naka don samun dama zuwa ɗaya.
Mai tunin Aminci
Mun sani zai iya zama mai wuya yin rikodin ganawa1 da mutane. Maiyuwa ba zasu ji daɗin yin magana game da rayuwarsu ba. Kuma maiyuwa ba zaka ji daɗin yi musu tambayoyi ba. Wasu lokuta, magana game da abubuwa zai iya taimakawa mutane jin rangwamen kaɗaici, da sanya rayuwarsu mai saukin fahimta. Shugabantar ganawa don labarai shima zai iya taimakon mutane jin kusanci da juna.
Ko yaya, koyaushe kayi tunanin abubuwa kamar lafiya da keɓantawa lokacin ganawa da mutane don labaransu. Anan akwai wasu abubuwa don tunawa:
- Tabbatar da wanda zaka gana dashi yasan abinda kake shirin yi da labarin (kamar yadda, cewa kana yin rikodin ta, kuma cewa wasu mutane maiyuwa su ji).
- Tabbatar da masu shiga sun san cewa basu da buƙatar amsa tambayoyi masu ciwo ko waɗanda maiyuwa su haifar da fallasa bayani mai mutunci. Duk labaran za'a bada su da ganin dama.
- Idan wanda kake ganawa dashi yana bada wani bayani wanda zai iya sanya su ko iyalansu ko abokansu a hɗari, tsaida rikodin ka fara ganawar da farko, ka sa su maimaita labarin ba tare da waɗancan cikakkun bayanan ba.
A wasu halayen, maiyuwa ka so kare asalin mai bada labari naka ta ƙin yin rikodin sunansa ko sunanta. Anan gawasu misalai na wasu magana masu mahimmanci inda zai zama babu aminci a raba sunan mutumin da kake ganawa dashi:
- Labari wanda yake da alaƙa da ciwan ƙanjamai na wani mutum.
- Labarai waɗanda suke da alaƙa da sujojin yaro, yara a mahalli, ko yara a bayan kanta mai kariya.
- Tattaunawa a kan azaba na jima' i ko ci da gumin mutane.
- Tattaunawa akan tuhumar wani ko samu da laifi.
- Magana mai ƙarfi akan siyasa ( inda kana zaune awurin haɗarine a faɗi irin waɗannan abubuwa cikin jama'a).
ƙarin Albarkatu
Muna burin wannan jagora mai amfanine ga ɗalibai da malmaiwurin gano duniyar labarin baka da bada labri na sirri. Aƙasa akwai ƙarin albarkatu don taimakonka wajen gano ƙari gameda hanyoyi da zasu taimak kiyaye labarunka - kamar Labaru Namu.
Ziyar gidan yanar sadarwa namu a www.ourstories.org.
Saboda binciken ganawa, ƙarin sawara saboda tambayoyi da wasu bayanin masu taimako, duba Labari Namu Jagorar Ganawa na Baligi a . www.ourstories.org/adultguide.html.
Koyi ƙari inda zaka sarrafa ganawa a StoryCorps' yi shi da jagora na kanka . http://www.storycorps.net/record-your-story/cant-come-to-us/diy-guide.